Ba Zan Daina Rusau Da Korar Ma’aikata A Kaduna Ba – El-Rufa’i

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamna Nasir El-Rufai ya ce ba zai gaza ba wajen cigaba da sallamar ruba-ruban ma’aikata da kuma rushe gine gine ba har zuwa ranar karshen wa’adin mulkin sa. 

Gwamnan, ya baiyana haka ne a yayin taron kaddamar da wani littafi da aka wallafa akan irin kokari da ya yi a kan kujerar sa ta gwamna, a lokacin da ake sauran kwanaki kadan ya bar kujerar. 

Littafin dai mai taken “Putting People First” ma’ana, ‘amfanar da al’uma shine mulki’, wani gogaggen dan jarida kuma mai sharhi a kan lamuran yau da kullum Mista Emmanuel Ado ne ya wallafa. 

Gwamna El-Rufai ya ci gaba da cewa ya yi kokarin barin baya da kyau a dukkanin tsare tsaren da ya yi na jagoranci a jihar. 

Related posts

Leave a Comment