Ba Za Mu Lamunci Tozarta Arewa Ba – Gwamnonin Arewa

?ungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa 19 sun yi tir gami da Allah wadai a kan ?azamar zanga-zangar EndSARS wadda ta gudana a sashin Kudancin Najeriya, da kuma sauran al’amura da za su tayar da tarzoma, inda suka ?alubalanci masu neman biyan wata bu?ata su bi tsari na Zanga-Zangar lumana ba tashin hankali ba.

Gwamnonin sun tabbatar da cewa ko ka?an ba zasu lamunci dukkanin wani tozarta yankin arewa ba, sannan suka roki mutane da su hada kai da nuna kaunar juna tsakanin ‘yan Najeriya baki ?aya.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin takardar bayan taro da kungiyar Gwamnonin ta fitar a babban taron da suka yi da Sarakunan Arewa a fadar gwamnatin Jihar Kaduna.

Sakataren Gwamnatin tarayya, Shugaban ma’aikatan fadar Shugaban Kasa, Shugaban Majalisar Dattawa, Kakakin Majalisar wakilai, Shugaban ‘yan sanda, Ministoci, Manyan Sarakunan Arewa da sauran manyan mutane sun samu damar halartar taron.

Takardar bayan taron wadda Shugaban ?ungiyar gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya karanto, ta kunshi abubuwa da dama wadanda za a yi domin kawo cigaba a Jihohin Arewa 19.

Gwamnonin sun yaba gami da jinjina ta musamman ga Sarakunan Yankin Arewa ?ar?ashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’adu Abubakar, a kan rawar da suka taka wurin dakatar da matasan arewa daga shiga zanga-zangar EndSARS.

Sun tattauna yadda za su kawo hadin kai da cigaba a kasa. Sannan sun tattauna a kan yadda mutane ke yada labaran bogi a kafafen sada zumuntar zamani.

Sun tattauna a kan yadda za a sanya ido a babban birnin tarayya don gudun cigaba da lalata dukiyoyin gwamnati. Sannan sun shawarci majalisar dattawa da su dinga hanzarin dakatar da duk wata zanga-zanga a cikin kasa.

Kuma sun tattauna bukatar yin zaman gaggawa domin samun daidaitawa ?ungiyar Malaman Jami’o’i ASUU don dalibai su koma makarantunsu.

Related posts

Leave a Comment