An bayyana cewar ko ka?an jama’ar Arewa ba za su lamunci cin mutunci da kisan da Inyamurai ke yi wa ‘yan Arewa a Kudancin Najeriya ba da sunan fashe haushi domin neman ?asar Biyafira.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin Shugaban ?ungiyar cigaban matasan Arewacin Najeriya na kasa Kwamared Kamal Nasiha Funtuwa, a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a garin Kaduna dangane da cigaba da kisan da tsagerun Inyamurai ke yi wa ‘yan Arewa a Jihohin su.
Kamal Funtuwa ya kara da cewar idan Inyamurai suna neman ?asar Biyafira ne to ba ta hanyar kisan ‘yan Arewa ba ne zai sa su samu biyan bukata, inda ya bada misali da kisan gillar da tsagerun suka yi wa tsohon Kakakin Majalisar dokokin Jihar Adamawa Ahmad Gulak a Jihar Imo, abin da ya bayyana da babban takaici.
“Ya kamata tsagerun Inyamurai su sani cewa da akwai tsagerun da suka fi su iya tsageranci a arewa, sannan su sani akwai Inyamurai da yawa dake rayuwa a Arewacin Najeriya a duk lokacin da aka ce za’a mayar da martani a Arewa abin ba zai yi musu Kyau ba”.
Dangane da kiran da kungiyar Dattawan Arewa ta ACF ta yi na cewar ‘yan Arewa su kauracewa shiga yankunan Inyamurai domin kariya daga dukiya da rayukan su, Kwamared Nasiha Funtuwa yace wannan kiran ai yazo a kurarren lokaci ne tun tuni ya kamata ayi shi, domin sanin halin rashin mutunci na Tsagerun Inyamurai ne ya sanya a baya gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya suka basu wa’adin ficewa daga yankin Arewa.
Shugaban matasan ya kuma yi tsokaci akan kalaman da shugaban kasa Buhari ya yi na fa?in cewar tura ta kai bango ba za’a amince da rashin kunyar tsagerun Inyamuran ba, inda yace kalaman Buhari abin dubawa ne domin a baya bai yi irin wannan kalamin ba, tun da a yanzu ya furta za’a zuba ido domin ganin matakin da zai ?auka.
