Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babban bankin Najeriya CBN ya ce ba gudu ba ja da baya game da wa’adin da ya sanya na daina amfanin da tsoffin takardun ku?in ?asar daga ranar 31 ga watan Janairu.
Gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele ne ya bayyana haka bayan ganawar kwamitin babban bankin kan tsare-tsaren ku?i.
Mista Emefiele ya jaddada cewa babban bankin ya bayar da wadataccen lokaci ga ?an ?asar da su mayar da tsoffin ku?adensu zuwa bankunan ?asar domin musanya su da sabbi.
Gwamnan babban bankin ya ?ara da cewa tun bayan sauya fasalin takardun ku?in uku an samu raguwar garkuwa da mutane domin kar?ar ku?in fansa.
Ya ?ara da cewa kawo yanzu babban bankin ya kar?i tsoffin takardun ku?i da adadinsu ya kusa naira tiriliyan 1.5, tare da fatan cewa za su iya kai wa tiriliyan biyu kafin cikar wa’adin da bankin ya saka.
”Mutane na ci gaba da ri?e ku?i tare da ajiye su a gidajensu, alhalin ba su da izinin yin hakan, kuma suna amfani da su wajen ya?a jita-jita game tsoffin takardun ku?in” in ji Emefiele.
Ya ci gaba da cewa: “Mun ro?i Hukumar ya?i da yi wa tattalin arzikin ?asa ta’annati ta EFCC da hukumar ya?i da almundahanar ku?a?e ta ICPC da kada su matsa wa mutane, kuma bisa alfarmar da na ro?a ba za su yi hakan ba”.
?an Najeriya da dama na ?orafi game da ?arancin sabbin takardun ku?in, suna masu cewa har yanzu bankunan ?asar na bai wa kwastomominsu tsoffin takardun ku?i a yayin da ya rage ?an kwanaki kafin ?arewar wa’adin da babban bankin ya bayar ya cika.
