Ba Za Mu Iya Rage Farashin Gas Ba – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bayyana cewa lamarin tsadar gas ?in girke-girke ya fi ?arfin ta, ba za ta iya saukar da farashin tsadar da ya yi ba.

Gwamnati ta ce dalili shi ne gas ?in girke-girke ba ya cikin man da gwamnatin tarayya ke biya wa ku?a?en tallafi.

“Saboda kasuwannin duniya ke daidaita farashin gas ?in girke-girke, kuma ba ya cikin man da ake biya wa tallafi.”

Karamin Ministan Fetur Timipre Sylva ne ya bayyana haka, ganin yadda ‘yan Najeriya ke fama da matsin-lambar tsadar gas, har ta kai akasarin gidaje yanzu an koma girki da gawayi ko itace da ?iraruwa.

Sai dai kuma Sylva ya ce amma gwamnati za ta duba ta ga ko akwai wani abu da za ta iya yi a kan lamarin.

Hukumar Kula da Makamashi ta Duniya (International Energy Agency) ta ce tsadar farashin gas a Turai na da nasaba da farfa?owar da tattalin arzikin ?asashe ya fara yi, bu?atar sa da ake yi a yanzu fiye da wanda ake samarwa, sai kuma matsanancin sanyin hunturu da ake yi a wasu sannan Turai.

Cikin shekara dai farashin gas ya nunka fiye da sau ?aya a Najeriya, har ta kai gidaje da dama sun daina amfani da gas, sun rungumi gawayi da ?iraren itatuwa.

Yayin da Sylva ke amsa tambayoyin manema labarai a ranar Talata a Fadar Shugaban ?asa, ya ce wani dalili da ya ?ara haddasa tsadar gas a cikin Najeriya, shi ne harajin-jiki-magayi (VAT), wanda aka ?ora a kan gas.

Related posts

Leave a Comment