Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya karyata rade-radin da ake ta yadawa musamman a wasu kafafen yada labarai cewa wai yana maular a yi masa shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa a sabuwar gwamnati mai zuwa.
Gwamna El-Rufai ya fa?i haka ne a garin Gombe, a wajen kaddamar da wasu manyan ayyuka da gwamnan jihar Yahaya Inuwa yayi.
Gwamna Inuwa ya gayyaci El-Rufai ya kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar take yi da wadanda ta kammala.
Sai dai kuma bayan haka da yake zantawa da manema labarai a garin Gombe, El-Rufai ya karyata rade-radin da ake ya?awa wai yana neman a na?a shi mukamin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Tinubu idan aka rantsar da sabuwar gwamnati ranar 29 ga Mayu.
El-Rufai ya ce ” Ba mu ta?a zama ni da za?a??en shugaban kasa mun yi irin wannan tattaunawa ba. Ni a ganina ba sai ka na cikin gwamnati ba ne za ka iya bada gudunmawar ka don cigaban kasa, ko daga can inda kake ma zaka iya bada gudummawar ka.
” Nan da kwanaki 22 bayan mun mika.mulki, hutu kawai make bukata ka’in da na’in. Sannan kuma mu maida hankali wajen bada kowacce irin gudunmawa da zamu bada don ci gaban kasa baki daya.
” Idan gudunmawa don ci gaba ake so, a kowani bangare kake zaka iya bada Irin taka, komai ?an?antanta kuwa.
A karshe El- Rufai yayi wa ?an Najeriya albishir cewa Bola Tinubu ba zai ba mara?a kunya ba, sannan kuma ba za ata?a yin da na sani ba da za?en sa da aka yi, yan Najeriya za su yaba masa matuka.
