Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa sohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa na cikin tsoffin gwamnonin 1999 da suka gana da Shugaba Tinubu.
A hirar sa da BBC, ya ce duk wani mai mulkin da zai kai wa ziyara, zai je ne ba don neman wani mu?ami a wajensa ba.
*Ban ziyarci Tinubu domin neman wani mukami ba kuma ba Mukami bane a gabana, na amsa gayyatar sa ne bisa neman da ya yi mana.
A makon da ya gabata ne shugaban ?asa Tinubu ya gana da tsofaffin gwamnoni na shekarar 1999 a fadar shugaban kasa shekarar da shi ma ya yi Gwamna a Legas, lamarin da ya sa jama’a surutai.
