Ba Kwankwaso Bane Ya Fadi A Wajen Kamfen – NNPP

A wani bidiyo da ya ke yawo a kafafen sadarwa na zamani da wani mai amfani da Facebook ya wallafa, ana iya ganin wani mutum da ake zargin cewa wai ?an takarar shugabancin kasa ne na jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso ya tuntsuro daga munbarin kamfen.

Mai amfani da Facebook din ya yi rubutu tare da bidiyon kamar haka: “Daga karshe ya ga sakamakon rashawa. Na yi imanin an ware kudi mai yawa don gina mimbarin amma wanda aka bawa aikin ya yi aiki mara kyau ya soke sauran kudin a aljihunsa. Ga sakamakon hakan.

A bidiyon da ke yawon, an hangi mutumin da aka ce wai Kwankwaso ne ya hau wani katako inda ya yi yunkurin gyarawa, jim kadan, shi da sauran yan jam’iyya suka fadi bayan katakon da ke mimbarin ya rushe. Nan take wasu yan jam’iyya mafi yawancinsu sanye da jan hula, mabiyan Kwankwaso, suka taya shi ya tashi.

A Twitter da sauran shafuka da dama sun wallafa bidiyon da rubutu daban-daban da ke nuni da cewa Kwankwaso ya fadi daga mimbari. Kazalika, kafafen watsa labarai kamar Pulse, WithinNigeria, da 247ureports, da wasu sun wallafa rahoton, suna ikirarin Kwankwaso ne ya fadi wurin rali.

tantancewa TheCable ta saka bidiyon a InVID, manhajar tantance bidiyo, nazarin da aka yi na hoton bidiyon ya nuna mutumin da ya fadi ba shi da kamanceceniya da Kwankwaso.

Mutumin da ake cewa Kwankwaso ne, sunansa Maliki Kuliya, tsohon kwamishinan shari’a na Kano, yana cikin manyan ?usoshin tafiyar kwankwasiyya amma ba Kwankwaso bane.

An kuma tuntubi Abdullahi Rogo, kakakin NNPP don tabbatarwa idan dan takarar shugaban kasar jam’iyyar ne a bidiyon da ya bazu. Rogo ya ce: “A’a, karya ne. Ba Kwankwaso bane.”

Related posts

Leave a Comment