?an takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya sanar da bayar da gudummuwar Naira miliyan 50 ga ‘yan gudun hijira wa?anda matsalar tsaro ta tarwatsa a Katsina.
Atiku ya bayar da tallafin ne a lokacin da ya ziyarci mai martaba Sarkin Katsina Dr Abdulmuminu Kabir Usman a fadarsa a wani bangare na yakin neman zabensa.
Atiku ya je fadar ne domin neman shawara da addu’a da albarka daga wajen Basaraken a yunkurinsa na zama shugaban kasar.
Ya ce ya damu da matsalolin rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki da ke damun sassan kasar nan, ya kuma yi alkawarin mayar da hankali a kansu idan aka zabe shi.
A martanin Sarkin ya ce ya ga haske a yunkurin Atiku na zama shugaban Najeriya a 2023, ya ce ya ji dadin yadda dan takarar shugaban kasar ya yi alkawarin magance matsalar rashin tsaro da tattalin arziki, wadanda ya ce su ne batutuwan da suka kai shi asibiti kwanan nan.
Ya yi addu’ar Allah ya sa a yi zabe cikin nasara da kwanciyar hankali a 2023, inda ya ce kasar nan ta kowa ce ba tare da la’akari da kabilanci ko addini ba.
Daga fadar Sarkin, jirgin yakin neman zaben ya koma gidan Iyalan ‘Yar’aduwa domin gaishe da Hajiya Dada, mahaifiyar marigayi Shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua, sannan ya nufi filin wasa na Muhammadu Dikko Katsina, inda aka gudanar da gangamin yakin neman zaben.
