Atiku Ya Bada Shawarar Dawo Da Tsoffin Soji Bakin Daga

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma ?an takarar shugabancin ?asar Atiku Abubakar ya yi kira da a kawo ?arshen matsalolin tsaro a Najeriya cikin gaggawa.

A wasu jerin sa?onni da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Atiku ya ce talakawan Najeriya na rayuwa cikin fargaba da ?ar-?ar.

Ya ce babu inda ke da tsaro a ?asar, ba a makaranta ba, ba a kasuwa ba, ba kuma a gonaki ba, ba masallatai ba kuma ba coci-coci ba

Atiku ya ce abin takaici ne yadda masu ta da ?ayar baya ke sa?a?owa daga yankin arewa maso gabashin Najeriya suna shiga jihohi kamar jihar Neja wadda ke ma?wabtaka da babban birnin ?asar.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta duba yiwuwar yi wa tsoffin jami’an tsaro kiranye su dawo bakin daga don taimakawa wajen ya?i da masu ta da ?ayar baya.

Atiku ya ce Najeriya za ta iya koyi da ?asashe kamar Lebanon da Liberia da Saliyo da suka yi wa tsoffin sojojinsu kiranye kuma suka amsa don yi wa ?asarsu hidima.

Sannan ya shawarci gwamnatin tarayya kan ?ara wa jami’an tsaro albashi inda ya ce hakan zai ?ara masu ?warin gwiwar yin ya?i bin ha??i da gaskiya.

Related posts

Leave a Comment