Atiku Cikakken Makaryaci Ne – Tsohuwar Ministar Ilimi

Tsohuwar ministar ilimi a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo Oby Ezekwesili ta bukaci Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP ya daina yi wa mutane ‘karya’ a yayin ya?in neman za?e.

Tsohuwar ministar ta furta hakan ne yayin martani kan ikirarin da tsohon shugaban kasar ya yi a shafinsa na Twitter na cewa shine ya jagoranci tawagar tattalin arziki karkashin gwamnatin Obasanjo.

Obi, wacce ta yi aiki a matsayin minista yayin da Atiku ke mataimakin shugaban kasa karkashin gwamnatin Obasanjo tsakanin 1999 zuwa 2007, ta ce dan takarar na PDP bai taba zama shugaban tawagar tattalin arziki na Obasanjo ba wato (EMT).


Atiku, a shafinsa na Twitter a ranar Talata 17 ga watan Janairu, ya bayyana cewa shine shugaban tawagar tattalin arziki na gwamnatin Obasanjo. Ya ce: “A matsayi na na shugaban tawagar tattalin arziki, lokacin ina mataimakin shugaban kasa, na taka rawa sosai wurin tsara shirin farfado da bangaren yan kasuwa da neman a bawa masu saka hannun jari damar shigowa a dama da su wurin gina tattalin arziki. Kuma mun samu nasarori sosai.”

Da ta ke martani kan ikirarin, tsohuwar ministan ta ce Atiku bai taba shugabancin tawagar kula da tattalin arziki ba a gwamnatin Obasanjo, tana mai kira ga dan takarar na shugaban kasa na PDP ya daina yaudarar mutane.

Related posts

Leave a Comment