Jam’iyyar APC ta rasa daya daga cikin yan takararta na gwamna a jihar Kaduna, Sani Sha’aban Sha’aban wanda suruki ne ga shugaban kasa Buhari ya rasa tikitin takara a hannun Sanata Uba Sani.
A ranar Litinin, 28 ga watan Nuwamba, Sha’aban ya sanar da ficewarsa daga APC a cikin wata wasika da ya sanyawa hannu, kuma aka rarraba ta ga manema labarai.
Ya ce harkokin jam’iyyar ne suka sanya shi yin murabus, yana mai zargin cewa maimakon shayar da mutane romon damokradiyya, wasu yan tsiraru a APC reshen Kaduna sun kwace tsarin jam’iyyar.
“A inda ra’ayoyin yawancin mutane bai da wani muhummanci. Ba zan iya ci gaba da kasancewa a jam’iyyar da bata damu da rayuwar mutane, zaman lafiya da mutunta al’ada ba.
“Ni Sani Mahmood Sha’aban na yi murabus daga matsayin dan APC a dukkan matakai a hukumance a yau 28 ga watan Nuwamban 2022.”
Sha’aban ya ce yanzu yana tattaunawa don daukar mataki na gaba, cewa zai sanar da jam’iyyar da zai koma nan ba da jimawa ba. Ya ce zai ci gaba da kalubalantar dan takarar gwamnan APC a kotu duk da cewar ya fice daga jam’iyyar.
