Kungiyar Gidajen Ya?a labarai masu zaman kansu na ?asa (IBAN) sun zabi Alhaji Ahmed Tijjani Ramalan a matsayin sabon shugaban riko na kungiyar.
Hakan ya biyo bayan ?arewar wa’adin shugabannin kungiyar a yayin wani taron gaggawa da suka gudanar ranar Laraba 17 ga watan Afrilun 2024.
Taron ya bayyana an Sir Godfrey Ohanbuwa a matsayin shugaban kwamiti na musamman da zai jagoranci ganawar ?ungiyar da bangaren Gwamnatin tarayya domin tattaunawa da lalubo hanyoyin magance matsalolin da kungiyar ke ciki.
Da yake mayar da jawabi sabon shugaban rikon ?ungiyar Alhaji Ahmed Tijjani Ramalan ya bada tabbacin yin dukkanin mai yiyuwa wajen kawo karshen matsaloli da manyan kalubale da gidajen ya?a labarai masu zaman kansu ke fama dasu a Najeriya.
