An Sallami Matuka Jirgi Sakamakon Ba Hammata Iska A Sararin Samaniya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin Paris na ?asar Faransa na cewa an sallami wasu matu?a jirgin saman kamfain Air-France biyu sakamakon gwada ?wanji da suka yi cikin jirgi.

Matu?in jirgin da mataimakinsa sun ba hammata iska yayin da suke tu?a jirgi ?irar Airbus A320 daga Geneva zuwa Paris a watan Yuni kamar yadda jaridar Swiss News Outlet ta shaida.

Ma’aikatan jirgin sun shiga tsakani inda ?aya daga cikin ma’aikatan ya tsaya tare da matu?a jirgin har sai da jirgin ya sauka ba tare da matsala ba.

Fa?an nasu dai bai shafi sufurin jirgin ba, a cewar kamfanin jirgin.

Lamarin kuma ya faru ne bayan wallafa wani rahoto da hukumar da ke bincike kan sufurin jiragen sama ta Faransa ta yi ranar Talata da ya ce kamfanin jirgin yana sako-sako game da tsare-tsarensa na tsaro.

Related posts

Leave a Comment