An Kai Hari Ofisoshin Mu Sau 41 Cikin Shekaru Biyu – INEC

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya yi gargadin cewa yunkurin kawo hargitsi a harkar zabe na iya lalata demokradiyyan Najeriya da kuma rikita kasar gaba ?aya.

Yakubu ya bayyana hakan ne a taron gaggawan da yayi da hukumomin tsaro a Abuja ranar Alhamis kan hare-haren da ake kaiwa ofishoshin hukumar musamman a yankin kudu maso gabas.

Yakubu yace, “Ko shakka babu hukumar ta shiga wani hali a yan makwannin da suka gabata. Yadda ake babbaka ofishoshin hukumar da lalata dukiyarta babban kalubale ne ga shirye-shiryen zaben da mukayi.”

“A shekaru biyu da suka gabata, an samu hare-hare 41 ciki har da wadanda aka kai da gayya. Guda tara a 2019, 21 a 2020.”

Ofishoshi 11, motoci 13, da Janareto 429 mukayi asara a hare-hare 41 da aka kai mana ba ?aukautawa. “A makwanni hudu da suka gabata, an kona ofishoshin hukumar 11 kuma an sace kayayyaki. Biyu ciki harin Boko Haram da tsagerun yan bindiga ne yayinda 11 na yan tsageru da yan bangan siyasa ne, ”

Farfesa Mahmoud ya kara da cewar “A lokacin zanga-zangan EndSARS a Oktoban bara, an kai hare-hare 18, yayinda wasu yan tsageru suka kai 11.”

Related posts

Leave a Comment