An Kafa Kwamitin Gano Masu Sayar Da Kadarorin Da Aka Kwace Hannun Barayin Gwamnati


Ministan Shari’a Abubakar Malami ya kafa Kwamitin Banka?o Wa?anda Su Ka Fara Sayar Da Kadarorin Gwamnatin Tarayya, wa?anda aka ?wato daga hannun ?arayin gwamnati.

Kafa kwamitin ya biyo bayan ?ullar wasu rahotanni a jaridu da su ka ce wasu a cikin Ma’aikatar Harkokin Shari’a sun fara sayar da kadarorin da gwamnatin ta ?wato a ?oye ta ?ar?ashin ?asa.

Cikin wata takardar da Kakakin Malami ya raba wa manema labarai a ranar Talata, ya ce, “Ministan Shari’a Abubakar Malami bai bada iznin a fara sayar da kadarorin ba. Kuma idan ma har wasu sun aikata laifin sayar da wasu daga cikin kadarorin, to ba da iznin sa ba.”

Gwandu ya ce a kan haka Malami ya kafa Kwamitin Mutum 5, da za su binciko tare da gano wa?anda ke da hannu wajen sayar da kadarorin, idan har an sayar da wasu ?in.”

Kwamitin na ?ar?ashin shugabancin Daraktan Shigar Da ?ararraki na Tarayya (DPP), sai kuma Babban Sakatare a Ma’aikatar Shari’a a matsayin sakataren kwamiti.

An bayar da mako ?aya duk mai wata hujja ko ?arin haske kan wannan zargi, to ya gaggauta aikatawa a Ofishin DPP ko Ofishin Babban Sakataren Ma’aikatar Shari’a, daga ranar 1 Ga Disamba zuwa 7 Ga Disamba.

“Kwamiti zai bincika ya gano idan har an fara sayar da kadarorin ta ?ar?ashin ?asa.

“Idan ya gano an fara, to zai banka?o duk wani ko wasu masu hannu a cikin wannan har?alla.

“Kadarorin da za’a yi binciken a kan su, sun ha?a da gidaje, maka-makan filaye, motocin alfarma, tankokin jiragen ruwa na ?aukar dakon fetur, masana’antu da manyan injinan sarrafa kayayyaki a cikin masana’antun da gwamnati ta ?wace.

Related posts

Leave a Comment