An Kaddamar Da Rundunar ‘Yan Sanda Ta Operation Dawo Da Zaman Lafiya Dole

Babban Shugaban Rundunar ‘yan Sanda ta ?asa Usman Al?ali Baba, ya ?addamar da sabuwar rundunar yan sanda da akai wa take da ‘Operation dawo da zaman lafiya dole’ a jihar Enugu dake kudancin Najeriya.

Sabuwar rundunar zata yi ya?i ne a yankin kudu maso gabashin ?asar nan domin dawo da cikakken zaman lafiya a yankin.

An gudanar da taron ?addamar da rundunar a ranar Talata a Micheal Okpara Square dake birnin Enugu, babban birnin jihar ta Enugu.

Daga cikin wa?anda suka halarci taron kaddamarwan akwai gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi. Wannan na zuwa ne kwana biyu kacal bayan wasu yan bindiga sun kai hari Hedkwatar hukumar za?e INEC a jihar Enugu, inda suka ?ona motoci da wasu kayayyaki ranar Lahadi.

Rahotonni sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun ?ona motoci shida a harin da suka kai ofishin INEC ?in na jihar Enugu. Hakanan kuma a watan Afrilu, yan bindiga sun kashe jami’an yan sanda biyu a harin da suka kai ofishin Adani, karamar hukumar Uzo-Uwani jihar Enugu.

Related posts

Leave a Comment