An Gudanar Da Bikin Mashaya Rake A Birnin Kano

‘Ya’yan ?ungiyar mashaya rake dake Unguwar Dorayi Karama, unguwar Bello sun shirya gami da gudanar da bikin shan rake na musamman a Birnin Kano Jalla Babbar Hausa.

An ruwaito cewa wannan shine karo na biyu da Kanawan suka gudanar da irin wannan biki na Mashaya Rake inda ake nuna bajintar shan rake babu ?a??autawa a tsakiyar birnin na Kano.

A hirar da matasan sukayi da manema labarai a birnin Kano, sun bayyana cewa sun shirya bikin ne musamman domin murnar sabuwar shekarar 2021 da aka shiga da kuma bikin daurin auren wasu daga cikin ‘yan unguwar.

Bikin shan raken ya yi matukar ?ayatarwa, inda dimbin jama’a suka halarci wurin da aka yi wannan sha’ani, cikin nisha?i da walwala tare da fata gami da addu’ar Allah maimaita na ba?in ba?a?a.

Jihar Kano da ke yankin Arewa maso yammacin Najeriya ta kasance Jihar da ta yi fice wajen kasuwanci da sauran harkoki na cigaban rayuwa, inda har kirari ake yi mata Kano Ko Da Me Kaje An Fi Ka!

Related posts

Leave a Comment