Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Gombe na bayyana cewar Gwamnan Jihar Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce Kamfanin Man Fetur na NNPC ta hannun wani kamfani mai neman man fetur ya gano danyen man fetur fiye da ganga biliyan 6 a yankin Kolmani.
Gwamnan ya bada tabbacin cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin ganin an fara hako danyen man da aka gano a masarautar Pindiga ta Jihar Gombe, nan ba da jimawa ba.
Inuwa ya bayyana hakan ne yayin wata liyafa da aka shirya domin karrama alkalin alkalai na wucin gadi na jihar Gombe, Hon Justice Muazu Abdulkadir Pindiga da aka yi a Pindiga a karamar hukumar Akko a ranar Asabar.
Ya ce sau da yawa ya kai ziyara hedkwatan hukumar NNPC kuma ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari don ganin yadda jiharsa za ta fara amfana da man fetur da iskar gas da ke jihar.
Gwamnan ya ce ba domin annobar COVID-19 ba da matsin tattalin arziki da aka shiga a baya-bayan nan, Gwamnatin Tarayya ta kammala shirin fara hako fiye da ganga biliyan 6 na danyen mai a yankin, amma ya bada tabbacin zai cigaba da bada himman ganin an cimma hakan.
Babban bako a taron kuma tsohon ministan sufuri, Abdullahi Idris ya yi wa gwamnan godiya bisa jajircewa don ganin an mayar da hankali wurin nemo danyen mai a Kolmani masarautar Pindiga.
Sarkin Pindiga, Muhammad Seyoji Ahmed, a jawabinsa ya ce abin da ke kama da rashin jituwa tsakanin Jihohin Gombe da Bauchi kan filin hako danyen man na Kolmani ba zai janyo rikici tsakanin jihohin ba.
