An Gano Bakin Zare A Ganawar Majalisa Da Shugabannin Tsaro

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugabannin tsaro da na ‘yan Majalisar Dattawan sun yi wata tattaunawar sirri a zauren majalisar dokokin kasar da ke Abuja, domin lalubo hanyar magance matsalar tsaro.

Hafsoshin tsaron sun amsa gayyatar ‘yan majalisar ce domin bayyana musu halin da ake ciki game da ta?ar?arewar tsaro a fa?in ?asar.

Daga ?an majalisar har shugabannin tsaron ba su ba da cikakken bayani kan abubuwan da suka tattauna ba amma a wani sa?o da majalisar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce sun tattauna ne kan batutuwan tsaro da suka ha?a da fashin daji da ta da ?ayar baya da ta’addanci da kuma hanyoyin kawo ?arshensu a Najeriya.

Sai dai Sanata Ali Ndume, shugaban kwamitin da ke kula da harkokin soji a majalisar ya bayyana wa BBC cewa wannan ce tattaunawa mafi armashi da Majalisar Dattawan ta ta?a yi da shugabannin tsaro a Najeriya.

“Wannan tattaunawa ta yi armashi kuma mun fahimci juna sosai da shugabannin tsaron,” a cewarsa.

“Za mu ba da goyon baya a ba su dukkan abun da suke bu?ata don su kawo ?arshen wa?annan matsalolin tsaro,” in ji Ndume.

Sai dai ya ce ba zai bayyana ainihin abin da suka tattauna ba saboda sirri ne, ya ce akwai batutuwan da ba za a iya ambatowa ba.

Ya kuma ce majalisar ta gamsu da bayanan da shugabannin tsaron suka yi masu kuma za su taimaka masu da abubuwan da suke bu?ata.

Sanata Ndume ya ce akwai abubuwan da shugabannin tsaron suka bayyana wa majalisa da ba su ta?a sani ba dagane da matsalar tsaro a Najeriya.

“Bayanan sirri ne da ba zan iya fa?a ba amma a wannan tattaunawa mun yi masu tambayoyin da ba mu ta?a yi masu ba, kuma su ma sun ba mu amsoshin da ba mu sani ba,” in ji Ndume.

Ali Ndume ya ce mataki na gaba da za ?auka shi ne duba ?warya-?waryan kasafin ku?i sannan a ware wa shugabannin tsaro ku?in da suke bu?ata don yin aiki yadda ya kamata.

Sauran jami’an da ke amsa gayyatar sun ha?a da da shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta NIA da kuma na shugaban hukumar tsaron farin kaya wato DSS.

Bayan Sanata Ahmad Lawan ya gode musu bisa ayyukan kare tsaron ?asa a madadin majalisar sai suka shiga tattaunawar sirri da misalin ?arfe 11:21.

Suna wannan ganawa ne a yayin da Najeriya take ci gaba da fama da matsalolin tsaro daga kowacce kusurwa ta ?asar.

A arewa maso yammacin kasar ana ci gaba da fama da matsalolin masu garkuwa da mutane da ‘yan fashin daji, wadanda suke kashe mutane ko kuma su tilasta musu biyan kudin fansa.

Wannan matsala ta fi ?amari a jihohin Kaduna da Zamfara da Neja da kuma Katsina.

Al?aluma sun nuna cewa an sace ?alibai fiye da 800 daga watan Disamba zuwa yanzu.

Related posts

Leave a Comment