An Ba Kamfanonin Waya Lasisin Yin Lambobin Zama ?an ?asa

An ba wa kamfanonin sadarwa lasisin yin rajistar mutanen da ba su da Lambobin Shaidar zama dan Kasa don rage dumbin jama’a a ofisoshin Hukumar Kula da Shaidun Dan Kasa, in ji Hukumar NIMC.

Darakta-Janar na NIMC, Aliyu Aziz, ya ce wasu sauran kungiyoyi masu zaman kansu da na gwamnati su ma hukumar ta ba su lasisi don samar da NINs domin magance cincirindon jama’a a ofisoshin hukumar.

Wannan ya zo ne yayin da ma’aikatan hukumar suka fada a ranar Talata cewa Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Isa Pantami, ya kafa kwamiti don magance bukatun ma’aikatan NIMC.

Da yake amsa tambayoyi game da matakan da NIMC ta dauka dangane da korafin da ‘yan kasa da kuma cincirindon jama’a a ofisoshin hukumar, Aziz ya ce an bai wa kamfanonin sadarwa na wayar salula ikon bayar da lambobin na ainihi.

“Mun ba da lasisi ga kungiyoyi masu zaman kansu da na gwamnati da suka hada da telcos (kamfanonin sadarwa) don samar da wasu cibiyoyi,” kamar yadda ya bayyana a cikin sakon WhatsApp ga wakilin PRNigeria.

Related posts

Leave a Comment