Amurka Ta Tallafawa Najeriya Da Rigakafin CORONA Miliyan Hudu

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, ya ce tallafin riga-kafin wani bangare ne tallafin allurar guda akalla miliyan 25 cikin miliyan 80 da za a rabawa kasashen nahiyar Afurka.

Amurka ta mi?a alluran karkashin shirin Covax, inda aka mika ga jami’an gwamnatin Najeriya a babban birnin kasar Abuja.

Hukumomin Najeriya sun ce, ana fatan riga-kafin samfurin Moderna za su kara ?aimi wajen ganin an yi wa ‘yan kasar riga-kafin cutar korona.

Kawo yanzu kashi 1 cikin 100 na al’ummar kasar miliyan 200, aka yi wa rigakafin korona samufurin , da ita ma aka karba karkashin shirin Covax a watan Maris.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun karuwar masu kamuwa da cutar Korona a kowacce rana , kuma na sabon nau’in Delta.

Jami’ai a Najeriyar na cewa an shiga zagaye na uku na barkewar cutar a kasar.

Related posts

Leave a Comment