Allah Ya Yi Wa Jarumi Sani Garba SK Rasuwa

Allah Ya yi wa fitaccen ?an wasan fina-finan Hausa Sani Garba SK rasuwa a yau Laraba a birnin Kano, bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Wani fitaccen furodusa Abdul M Amart Mai Kwashewa ne ya tabbatar wa da BBC rasuwar ?an wasan.

Marigayin ya rasu ne a Asibitin Muhammadu Abdullahi Wase da ke Nasarawa a ranar Laraba da yamma.

“Sani SK ya kai kusan shekara uku yana jinya a tsattsaye, amma rashin lafiyar ta taso masa sosai ne a baya-bayan inda ya shafe mako biyar yana jinya a asibitin,” in ji Amart.

Amart ya ?ara da cewa tun asali cutar ciwon suga ce yake fama da ita, wacce daga bisani ta haifar masa da cututtuka irinsu ?oda da hanta da hawan jini.

A baya dai an sha ya?a jita-jitar rasuwar Sani SK, inda ya dinga musantawa da kansa ma a wasu lokutan.

“A ranar yau da ya rasu ?innan aka fara yi masa wankin ?oda,” a cewar Furodusa Amart, wanda shi ke tsaye a kan kula ?aukar nauyin kula da lafiyar marigayin.

Sani Garba SK ?an asalin unguwar Zage ne a cikin birnin Kano, kuma a baya kafin ya fara harkar fina-finai mai yabon Manzon Allah ne a ?ungiyar Usha’un Nabiyyu.

Kafin kwanciyarsa a Asibitin Nasarawa sai da ya kwanta a Asibitin Murtala da ke cikin birni.

Abdul Amart ya ce tuni aka tafi da gawar mamacin gida, kuma za a yi jana’izarsa a gobe Alhamis.

Related posts

Leave a Comment