Wani dan Majalisar dokokin tarayya a Najeriya ya ce akwai guraben aikin gwamnatin tarayya sama da dubu ?ari da ashirin amma shugaban kasar Muhammadu Buhari ya hana a cike su.
Honorabul Sani Bala Tsanyawa, wanda shi ne shugaban Kwamitin kula da Ayyukan gwamnati na Majalisar Wakilan Najeriya ne ya tabbatar da hakan a hirarsa da BBC Hausa.
Ya ce tun a shekarar 2019 ne Shugaba Buhari ya sanar wa majalisar dokoki ?aukar matakin a lokacin da ya je zaurenta domin gabatar da kasafin ku?i.
A cewarsa “Lokacin gabatar da kasafin ku?i da (shugaban kasa) ya kawo wa majalisa, yake fa?a cewa ya dakatar da ?aukan aiki a ‘mainstream civil service’ – wato ma’aikatan da ke a aiki a ma’aikatu na kwaryar aikin gwamnati.”
Ya ce tun da shugaban ?asar ya sanya wannan haramci ba a ?ara ?aukar aiki ba a irin wa?annan ma’aikatu.
Sai dai a cewarsa an bai wa wasu ma’aikatun gwamnatin damar daukar ma’aikata saboda dalilai masu ?arfi.
Bangarorin da aka yi wa rangwamen sun ha?a da na tsaro da lafiya – sakamakon barkewar annobar korona.
Ya kara da cewa “Daga shekara biyar a baya zuwa yau, bincikenmu ya nuna cewa ma’aikata dubu ?ari da talatin ne suka bar aiki.”
“Wasun su ko dai sun mutu, wasu kuma sun yi ritaya, wasu kuma sun samu wani aikin na daban sun bar na gwamnatin tarayya.”
Ya ce amma a tsawon wa?annan shekaru biyar bayan sanya haramcin, mutum dubu shidda da dari bakwai ne kacal gwamnatin tarayya ta ?auka aiki.
Sannan ya ce duk da haka har yanzu yawan guraben na kara yawa saboda a kodayaushe akan samu ma’aikatan da ke mutuwa ko ajiye aiki, to amma har yanzu ba a cire wannan haramci ba.
Sai dai ya ce akwai wasu hukumomin da a wani lokaci sukan dauki ma’aikata, kamar babban bankin Najeriya (CBN) da hukumar sadarwa ta kasa (NCC), amma ba a ma’aikatun kwaryar aikin gwamnati ba, wa?anda a turance ake kira ‘ministries’.
