Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar na III, ya bukaci dukkan kabilun Nigeria su cigaba da zama a matsayin yan uwan juna domin Allah bai yi kuskure ba da ya hada mu zama a matsayin kasa daya.
Da ya ke jawabi a matsayinsa na shugaba a wurin taron bada lambar yabo na shugabanci na 2020 a ranr Alhamis a Abuja, Sultan ya ce raba kasar ba zai magance matsalolin da kowace kabilar ke fama da shi ba amma hada kai tare a warware matsalar ce ta fi amfani.
“Idan muka rabu kowa ya kama gabansa, ta yaya za mu rayu? Allah bai taba kuskure ba kuma baya kuskure, wannan shine kaddararsa kuma ya kamata mu rungume kadarar.
“Hada mu a matsayin yan Nigeria ba kuskure bane kuma wannan shine abin da Allah ya so. Idan yana son wani abin daban da tuni ya yi don haka ya kamata mu rungumi addinan mu a matsayin musulmi da kirista.
“Dukkanmu mun san daga mahallici daya muke.” Sultan ya ce wadanda ke amfani da addini domin raba kan mutane ba za su yi nasara ba domin mutanen kasar ba za su biye musu ba. Ya kuma shawarci yan Nigeria su bada gudumawarsu don ganin an samar da tsaro a kasar.
