Adamawa: Gwamnati Ta Sha Alwashin Inganta Albashin Malamai

Gwamnati jahar Adamawa ta kudiri aniyar inganta albashin malamai dama wasu alawus alawus dinsu domin ganin an samu ingaceccen ilimi dama samun cigaban jahar da kasa baki daya.

Gwamnan jahar ta Adamawa Ahmadu Ummaru fintiri ne ya baiyana haka a lokacinda yake jawabi a wurin bikin ranan malamai ta duniya wanda aka gudanar a dandalin mahmudu Ribadau dake yola.

Gwamnan Ahmadu Fintiri yace gwamnatinsa zatayi dukkanin abinda ya dace domin inganta walwalan malamai a fadin jahar ta Adamawa baki daya.

Fintiri ya kuma kirayi malamain da su kara kaimi wajen gudanar da aiyukansu yadda ya kamata wanda a cewarsa hakan zaitaimaka wajen cigaban ilimi yadda ya kamata ba tare da wata matsalaba.

Gwamnan ya kara da cewa gwamnati zata aiwatar da bukatun malamai wanda a cewarsa malamai sune gishikin rayuwa wanda in an horar da malami daya tamkar ankarantar da duniyane.

Tunda farko a jawabinsa na maraba shugaban kungiyar malamai a Najeriya N U T shiyar jahar Adamawa kwamuret Rodney s Nathan ya yabawa gwamnan Ahmadu Umaru Fintiri bisa yadda ya baiwa ilimi muhimmanci a gwamnatinsa tare da kiran gwamnan da ya aiwatar da karin girma da akeyiwa malamai da karin albashi mafi karanci, kudin hutu da kuma na sifiri da dai sauransu.

Rodney Nathan ya kuma tabbatar da cewa malamai zasuyi dukkanin abunda ya dace domin ganin an samu cigaban ilimi a fadin jahar baki daya.

Ya kuma godewa membobin kungiyar ta N U T a jahar Adamawa bisa goyon baya da kuma hadin kai da suke baiwa shuwagabannin kungiyar musammanma a duk lokacinda ake gudanar da biki makamancin haka.

Shima anshi jawabi shugaban kungiyar kwadigo a Najeriya wato N L C shiyar jahar Adamawa kwamuret Emmanuel Fashe ya nuna farin cikinsa dangane da wannan rana tare da kiran gwamnan da ya duba tare da warware matsaloli da ma aikata suke fuskanta domin ganin suma sun samu walwala a tsakanin al umma.

Wasu malamai da suka zanta da muryar yanci sun baiyyana farin cikinsu dangane da wannan rana ta malamai da aka ware dimon tunawa dasu tare kiran da fatan za a warware musu matsaloli da suke fuskanta a yayi gudanar da aiyukansu.

Hukumar bukasa ilimi da al adu na majalisar dinkin duniya wato UNESCO ne dai ta aiyana rana biyar ga watan oktoba na kowane shekara da yaza ranan malamai ta duniya domin dubawa tare da warware matsalolin da malamai ke sukanta baki daya.

Related posts

Leave a Comment