Adamawa: An Yi Kira Ga Gwamnatoci Su Samar Da Kamfanoni Domin Rage Zaman Banza

An kirayi gwamnatin tarayya dana jihohi da suyi dukkanin abinda ya dace domin samarwa kasan nan kamfanoni wanda haka zai taimaka wajen samar da wadaceccen aikinyi a tsakanin matasa dake fadin kasan nan baki daya.

Alhaji Adamu jingi na yayi wannan kira a lokacin da yake zantawa da miryar yanci a birnin yola. Fadar gwamnatin jahar Adamawa.

Alhaji Adamu yace yazuwa yanzu Najeriya ta kwashe shekaru akalla sittin da daya da samun yancin kai amman haryanzu bata da kamfanonin da kasan zata dogara da su wajen samar da kayakin da za a iya yin amfani da su a cikin kasan nan.

Don haka ya kamata gwamnatin tarayya ta farka ta tashi tsaye wajen bunkasa harkokin kasuwanci a fadin kasan wanda acewarsa hakan zai kawo cigaba yadda ya kamata.

Ya kuma shawarci gwamnatocin jihohi da suma suna da rawa da zasu iya takawa wajen bunkasa kasuwacin ta fannoni daban daban.

Harwayau ya kirayi yan Najeriya dasu kasance masu yin adu oi a koda yaushe domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen matsalar tsaro a fadin kasan nan baki daya.

Related posts

Leave a Comment