Adamawa: An Shawarci Manoma Da Neman Ilimin Aikin Noma

An kirayi manoma a fadin Najeriya da su kasance masu neman ilimin harkokin noman zamani domin samun cigaban harkokin noma harma da bunkasa tattalin arzikin kasa baki daya.

Ko odinataon Agriculture Biotechnology kuma uwargidan shuhaban ma aikatan gidan gwamnatin jahar Adamawa Dr Rose Maxwell Gidado ce tayi wannan kira a zantawarta da manema labarai a yola.

Dr Rose tace yanzu noma ya zama sana a kuma ancewa noma yanke talauci don haka ya kamata al umma su maida hankali wajen run gumar harkokin noma yadda ya kamata, tare da neman sanin yadda ake gudanar da noman a zamunance wanda a cewarta hakan zai taimaka wajen samun cigaban harkokin noman a fadin kasan nan.

Ta kuma shawarci noman a fadin Najeriya da sukasance masu neman ingantattun iri domin shukawa a gonakainau wanda kuma hakan zaisa a samu wadaceccen abinci yadda ya kamata.

Dr Rose tace indai za a maida hankali wajen noma da kuma neman ilmin noman za a samu cigaba wanda hakan zaisa Najeriya ta rike kanta a fannin abinci tare kuma da samar da aikikyi a tsakanin matasa.

Harwayau ta shawarci manoman da fadada nomansu ta shuka iri daban daban kamarsu wake, shinkafa, masara, gyada,dawa, da dai sauransu.

Ta kuma kirayi gwamnatin tarayya dana jihohi da su taimaka wajen samarwa manoman inganceccen tsaro domin baiwa manoman damar wadatar da kasannan da abinci.

Don haka akwai bukatar taimakawa manoman musammanma wadanda ke yankunan karkara da kayakin noman yadda ya kamata kuma akan lokaci.

Dr Rose Maxwell Gidado ta shawarci matasa da su shga a dama dasu a bangaren noma wanda acewarta shiganau zaisa su samu aikinyi domin dogaro da kansu. Ba tare da wata matsalaba.

Ta kuma shawarci gwamnatin tarayya dama na jihohi da su kasance masu shiryawa manoman bitoci daban daban wanda yin hakan zai taimaka wajen samu cigaba a bangaren noma yadda ya kamata.

Ta kirayin yan Najeriya da su cigaba dayin adu o i akoda yaushe domin kawo karshen matsala tsaro a fadin kasan nan baki daya.

Related posts

Leave a Comment