Babban Shehin ?ari?ar Tijjaniya a Najeriya Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yi kira ga Shugabannin kasa, ‘yan siyasa da kuma Shugabannin addini da su ji tsoron Allah su tabbatar da adalci, su kuma cire banbancin addini ko al’ada tsakanin wadanda suke jagoranta.
Sheikh Dahiru Bauchi ya yi wannan maganar ne a Abuja, a wani taro, wanda aka dauki bidiyonsa mai taken Lisanul Faidha wato Muryar Musulunci, wanda ANEST da Blue Bells Promoters suka shirya.
Kamar yadda Sheikh Bauchi yace, “Ubangiji ya umarci duk wani shugaba tun daga gidaje, anguwanni, kananun hukumomi, har zuwa shugaban kasa da su kasance masu tabbatar da kwatanta adalci tsakanin mabiyansu don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.”
Ya kuma shawarci masu wa’azi da su tabbatar sun samar da zaman lafiya da juriya ta addinai mabambanta, da tabbatar da kiran zaman lafiya a tsakanin mabiya domin kai wa ga nasarar da ake nema.
Jagoran ‘yan ?ari?ar ya shawarci matasa da su nemi ilimi, domin ilimi shine gishirin zaman duniya, kuma shine kadai zai samar da cigaban al’umma.
