Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Mahmoud Gumi ya bada labarin tafiyar da ya yi zuwa sansanin wasu ‘yan bindiga a dajin jihar Zamfara.
Ganin yadda ake fama da matsalar rashin tsaro a Arewa maso yammacin Najeriya, babban malamin ya shiga inda ‘yan bindiga su ke, ya na lallabarsu, akan su rungumi matakin zaman sulhu ba ?aukar bindiga ba.
Da yake yi wa gwamnan Zamfara, Alhaji Bello Matawalle, bayanin abin da ya gani, Malamin ya bayyana cewa tsagerun ‘yan bindigan sun zama ‘yan ta’adda ri?a?ku fiye da yadda mai zato ke zato.
Dr. Ahmed Mahmoud Gumi ya bayyana haka ne ranar Alhamis, 4 ga watan Fubrairu, 2021, a gidan gwamnati da ke garin Gusau a gaban Gwamnan jihar Zamfara Alhaji Bello Matawalle.
Shehin Malamin ya ?ara da cewa rashin kula ne ya jawo wadannan mutane su ka zama gawurtattun ‘yan ta’adda. Babban malamin ya yi kira ga gwamnatoci a kowane mataki, su yi sulhu da wadannan mutane, a cewarsa za a shawo kan matsalar ne ta hanyar neman lalama.
“A mafi yawan sansanin da na ziyarta a Zamfara, na zo na fahimci cewa abin da yake faruwa ba komai ba ne, ta’addanci ne da tada-kayar baya.”
“Wasu su na da ra’ayin cewa a auka wa miyagun nan, a hallaka su, amma abin da muka fahimta shi ne, yawancinsu jahilai ne dake bukatar ilmi da wayar da kai”.
Sheikh Gumi ya ce ‘yan bindigan su na ta’adi ne saboda yawan kai masu hari da ‘yan sa-kai su ke yi da ‘yan banga a kusan kullum.
Kafin yanzu, idan za ku tuna, Ahmed Mahmoud Gumi ya ziyarci wasu ‘yan bindiga a yankin Abuja da Kaduna, inda ake fama da satar mutane da kashe-kashe.
A watan da ya gabata, Dr. Ahmed Gumi, ya ziyarci wasu rugage masu hatsari a kan hanyar Kaduna zuwa birnin tarayya Abuja, ya yi masu wa’azin addini.
A ra’ayin Dr. Gumi, jahilci da duhun kai ne su ke addabar Fulanin da ke zaune a wadannan wuraren.
