Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri da wasu gwamnonin arewa a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
An kira taron ne don tattaunawa kan matsalar tsaro data addabi jihohin arewa 19.
Yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron, gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce sannu a hankali zaman lafiya na dawowa yankin sakamakon tsarin tsaro da gwamnatin tarayya da na jihohi suka amince da shi.
A kan ganawar da shugaban kasa, gwamnan ya ce, “Mun tattauna batun tsaro, ba don jiha ta ba kawai ba, face yankin Arewa baki daya, saboda yadda matsalar ta yi kamari a yanzu.
A cewarsa “Na yi masa bayani kuma gwamnan Neja shi ma ya yi masa bayani, shugaban kasar ya tabbatar mana da cewa za a dauki mataki a kan abin da muka tattauna game da batun rashin tsaro. ”
