Wasu ‘yan bindiga sun kashe Dagacin Dogon Daji, Mallam Anja, da ke ?aramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna a arewacin Najeriya.
“Yan bindigar da ake zargin ‘yan fashin daji ne sun kai wa gidan dagacin hari kuma suka harbe shi, abin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take, a cewar gwamnatin jihar.
Kwamishinan Tsaro na Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce ana gudanar da bincike kan lamarin domin gano wa?anda suka aikata kisan.
Kwamishinan ya ce Gwmana Nasir El-Rufai ya bayyana alhininsa game da kisan kuma ya yi addu’ar Allah ya ji kan basaraken.
Kazalika, gwamnan ya mi?a ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin da kuma al’ummar Dogo Daji.
