Rahotanni daga fadar Shugaban ?asa dake birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Borno da a ranar yau Alhamis.
Hakan na ?unshe ne a wata sanarwa da gwamnan jihar Borno ya fitar mai sa hannun mai taimaka masa kan harkokin ya?a labarai Isa Gusau.
Borno ce jihar da ta zama hedikwatar ?ungiyar Boko Haram inda ake fama da hare-haren maya?an.
Gwamna Babagana Umara Zulum ya ro?i ?an jihar da su ba da goyon baya da fatan alheri a yayin ziyarar ta Shugaban.
“Ina sake gode muku kan goyon bayan da kuka bai wa gwamnatin nan. Ina godiya bga kowa da kowa, kan goyon bayanku da fatan alherinku da addu’o’i da kuma zamantowarku ?an ?asa na gari,” kamar yadda sanarwar ta ce.
Lokaci na ?arshe da Shugaba Buhari ya kai ziyara Borno shi ne ranar 12 ga watan Fabrairun 2020, inda har wani dandazon mutane suka yi wa shugaban ihun ”ba ma yi, ba ma yi”.
“Ina farin cikin sanar da ku cewa gwamnatin tarayya ?ar?ashin Shugaba Buhari ta kammala gina gidaje 4,000 cikin 10,000 da aka amince a gina wa ?an gudun hijira.
“Wasu daga cikin gidajen nan suna yankin Kaleri da Dalori da sauran wurare,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ?ara jaddada gamsuwarta kan yadda “gwamnatin Buhari ta shawo kan matsalar tsaron sosai, ba kamar yadda abin yake a baya ba.”
“Gina wa?annan gidaje ya ta’alla?a ne ga samun zaman lafiyar da aka yi a yankunan jihar Borno.
“Na san har yanzu muna fama da matsalar tsaro, amma kuma idan muka waiwaya baya za mu ga cewa an samu sau?i musamman a yadda a baya wasu yankunan ma ba a shigarsu,” in ji sanarwar.
Sai dai duk da wannan yabo da gwamnatin jihar Borno ta yi wa gwamnatin Buhari, masu sharhi na ganin da sauran rina a kaba sosai a ya?in da ake a ?o?arin da?ile ?ungiyar Boko Haram.
