Ministan ?wadago da Ayyukan Yi na Najeriya Dr Chris Ngige, ya ce Kundin Tsarin Mulkin kasar na shekarar 1995 ?ar?ashin mulkin Janar Sani Abacha, wanda ya yi mulki tsakanin shekarun 1993 zuwa 1998, shi zai fi dacewa da ?asar.
Da yake magana a gidan talbijin na Channels a ranar Litinin, ministan ya ce wa’adin mulki na shekara biyar karo guda kawai da kuma tsarin kar?a-kar?a shi ne kawai zai warware matsalar nuna bambanci.
“Na yi amanna a yau, da gobe, Kundin Tsarin Mulkin Abacha na 1995 da ya tsara kar?a-kar?ar mulkin shugabancin ?asa zuwa yankunan Najeriya shida, da wa’adin shekara biyar a karo ?aya kawai, zai magance dukkan matsaloli; da magance jin zafin ya?in basasa, da kuma jin zafin June 12,” kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
“A yanzu, wannan kundin tsarin mulki shi ne zai fi dacewa ga ?an Najeriya su yi amfani da shi nan da shekara 30 inda dukkan yankunan ?asar shida za su ?an?ani za?in shugabancin ?asar,” in ji shi.
Ngge ya kuma ce da hakan zai magance batun bambanci idan yankin Kudu Maso Gabashin ?asar ya samar da shugaban ?asa na gaba.
“Mutanen yankin suna ganin kamar an ware su, ba a yaba musu, ko dai don farfaganda ko kuma don an zuga su, wanda a yanzu hakan ba shi da amfani,” in ji Ngige.Article share tools
