Ana Binciken Likitoci Kan Sanadin Mutuwar Maradona

Wata bakwai bayan mutuwar fitattacen ?an kwallon Argentina, Diego Maradona, masu gabatar da kara sun fara yi wa likitocin da suka kula da lafiyarsa kafin ya mutu tambayoyi.

Tawagar ta ?unshi likitoci guda bakwai da suka kula da Maradona.

Wani kwamitin ?wararru da ke bincike kan mutuwar Maradona na son tabbatar da zargin cewa bai samu kulawar da ta dace ba tare da yin sakaci wanda ya kai ga mutuwar ?an ?wallon.

Shahararren ?an ?wallon na duniya ya mutu ne sakamakon bugun zuciya a watan Nuwamban da ya gabata yana da shekara 60, makwanni bayan an yi masa tiyatar magance toshe jini.

Daga cikin wa?anda ake yi wa tambayoyi har da likitan da ya yi ?an ?wallon tiyata da kuma likitansa.

Akwai kuma ma’aikatan jinya guda uku da wani likita da ke bincikensu.

(Ana sa ran ci gaba da binciken likitocin har zuwa ?arshen watan Yuli

Related posts

Leave a Comment