‘Yan Bindiga Sun Sace Mata 60 Da Kone Gari Kurmus A Zamfara

Rahotanni daga Gusau babban birnin jihar Zamfara na bayyana cewar ‘yan fashin daji sun sace wasu mata kimanin 60 a cikin wani samame da suka kai kan wasu kauyukka jiya (Talata).

A cewar wani ?an majalisar wakilan kasar daga yankin, an sace matan ne daga kauyen Manawa yayin da aka kashe mutane hudu a kauyukan Malele da Randa a Karamar Hukumar Maru.

Hon. Shehu Ahmed S. Fulani dan majalisa mai wakiltar yankin da lamarin ya faru a majalisar wakillan Najeriya ya shaida wa BBC cewa garuruwa da dama ne ?an bindigar suka ?one a harin.

Ya ce maharan sun tafi da matan ne bayan mazajensu sun gudu a lokacin da suka kawo harin.

Related posts

Leave a Comment