Ku Kashe Duk Wanda Aka Kama Da Makami A Zamfara – Matawalle Ga Jami’an Tsaro

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamna Bello Matawalle na jihar ya umarci dukkan mazauna jihar da su mika makaman da suka mallaka ba bisa ka’ida ba ga hukumar ‘yan sanda mafi kusa dasu a cikin kwanaki bakwai kacal.

Gwamnan ya bada wannan umarnin ne yayin saka hannu a wata takardar shela ga dukkan jihar Zamfara, kamar yadda hadiminsa a harkar yada labarai, Zailani Bappa ya sanar a ranar Laraba.

Kamar yadda takardar ta nuna, umarnin ya biyo bayan umarnin da shugaban kasa ya bada na harbe duk wanda aka kama da makamai ba bisa ka’ida ba a take, domin tabbatar da samun lafiya.

Takardar ta ce: “Domin tabbatar da karfin ikon da nake da shi, ni Dakta Bello Mohammed, ina bada wadannan umarnin. “Dukkan makamai dake hannun jama’ar jihar Zamfara ba bisa ka’ida ba, a mika su ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa a cikin kwanaki bakwai daga ganin wannan sanarwan.

Related posts

Leave a Comment