Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ofishin mataimakin shugaban ?asa Farfesa Yemi Osinbajo yace gasar neman tikitin takarar shugabancin ?asar nan a za?en 2023 yana da?a jan hankali, amma shi anashi ?angaren ba wannan bane a gabansa, abin da ya sanya a gaba shine sauke nauyin aikin dake ofishin shi.
Ofishin ya bayyana cewa mataimakin shugaban ?asa, Farfesa Yemi Osinbajo, bashi da niyyar yin takarar shugaban ?asa a yanzu. Kakakin mataimakin shugaban, Laolu Akande, shine ya fa?i haka a wani jawabi daya fitar ranar Litinin a babban birnin tarayya Abuja. Yace Osinbajo bashi da ala?a da wa?anda ke ya?in neman za?ensa a yanar gizo.
Akande yace: “An jawo hankalin ofishin mataimakin shugaban ?asa kan wani shafin yanar gizo mai suna supportosinbajo.ng, wanda yake kira ga yan Najeriya su shigo tawagar yan sa kai domin nuna goyon bayansu ga Osinbajo yayin da za?en 2023 ke gabatowa.”
“Bayanan wannan shafin yanar gizon da neman agajin da suke yi yana cigaba da jan hankalin masu amfani da dandalin sada zumunta na whatsapp, kuma suna fa?in cewa Osinbajo ya amince zai yi takara amma a ?oye.”
“Ofishin mataimakin shugaban ?asa bashi da wata ala?a da wannan shafin yanar gizo ko tawagar mutanen dake ?aukar nauyin shi, Osinbajo bai nuna sha’awar tsayawa takarar kowace kujera ba a za?en 2023.”
“Amma ya maida hankali wajen aikinsa na mataimakin shugaba a wannan gwamnatin wajen ?o?arin shawo kan duk wani abu daya taso a ?asa, da kuma kulawa ga yan Najeriya.”
