Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar easu yan bindiga sun harbe wani jigo a yankin Kudancin Jihar mai suna Mr. Christopher Madaki, tare da matarsa da kuma sirikarsa a garin Golkofa ta ?aramar hukumar Jema’a jihar Kaduna.
Kwamishinan tsaron cikin gida, Mr. Samuel Aruwan, shine ya sanar da haka a wani sa?o. Kwamishina yace: “Hukumar yan sanda ta jihar Kaduna da hedkwatar tsaro, sun aikewa gwamnatin jihar Kaduna rahoton kisan mutane uku yan asalin jihar.
“A bayanan da muka samu bayan faruwar lamarin, yan bindigan sun farmaki gidan Christopher Madaki, jigo a garin Golkofa karamar hukumar Jema’a suka harbe shi, tare da matarsa da kuma matar ?ansa (sirikarsa).”
“Daga baya aka tabbatar da mutuwar su, yayin da ?ansa, Clement Musa Madaki, ya tsira da muggan raunuka.”
Hakanan kuma, Mr. Aruwan ya ?ara da cewa rundunar soji ta ‘Operation Safe Haven’ sun sami wani rahoto na batan wani mutumi mai suna, Ngode Patrick Kambai, a ?auyen Mabuhu ?aramar hukumar Zangon Kataf.
