An za?i gidajen talabijin biyu daga yankin Arewacin Najeriya gidan talabijin na Liberty da Tozali matsayin wadanda za’a rin?a ganin a tauraron dan Adam na DSTV da GOTV.
Wannan ya biyo bayan ganawar da gamayyar Kungiyoyin Arewa suka yi da shugabannin dake kula da Kamfanonin DSTV da GOTV a Tarayyar Najeriya a ranar Alhamis.
Tun farko da yake ?arin haske akan ?orafin da gamayyar kungiyoyin suka yi na cewar babu tashar talabijin ta ‘yan Arewa a jadawalin tashoshin DSTV da GOTV babban Darakta na Hukumar kula da kafafen ya?a labarai na ?asa NBC Ishaq Modibbo Kawu ya bayyana cewar tashar Liberty tuni tana kan GOTV.
Ganawar tasu wadda aka yi a dakin zartarwa na hukumar, ya samu halartar manya daga hukumar ta NBC da manyan wakilai daga gamayyar Arewa da wakilai daga kamfanin na DSTV.
Sakamakon taron ya amince da sanya tashoshi biyu daga yankin Arewa a jadawalin DSTV wadanda suka ha?a da Liberty TV da kuma Tozali TV wadanda suka cika ka’idojin da ake bukata, kuma kofa a bu?e take ga sauran tashoshin Arewa wa?anda suka cika ?a’ida.
Matakin da kamfanin na DSTV ya ?auka ya biyo bayan ?orafin da gamayyar kungiyoyin Arewa suka yi ne na cewar Kamfanin ya yi watsi da tashoshin Arewa a jadawalin tashoshin dake kan tauraron dan adam duk da muhimmanci da suke dashi.
Gamayyar kungiyoyin sun koka dangane da hakan inda suka bayyana cewa rashin sanya tashoshin da ke magana da harsunan da Jama’ar Arewa ke amfani da shi ya taimaka wajen kara haifar da matsalar tsaro a yankin.
