Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya sanya hannu a wata yarjejeniya da wani kamfani mai suna Zipline a wani tsari na raba magani a asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya ta hanyar amfani da kananan jirage masu sarrafa kawunansu (drones).
A jawabinsa, Gwamna El-Rufai ya ce wannan kamfani na Zipline da ke Kasar Amurka wanda ke da reshe a Kasar Ghana ya zabi Jihar Kaduna ne don ganin irin yadda jihar ta dauki sha’anin kiwon lafiya da muhimmanci.
Gwamnan ya kara da cewa, “ wannan tsari zai taimaka mana wurin rarraba magani da alluran riga-kafi zuwa duk lunguna da sakunan da ke jihar nan musamman inda muke fama da matsalolin tsaro kamar Birnin Gwari.
Sannan wannan tsarin zai taimaka mana wurin samar da ayyukan yi ga matasanmu tunda a nan Kaduna za su rika kera wadannan jirage masu sarrafa kawunansu”.
