2023: Dole A Mayar Da Mulki Kudu – Sanata Gaya

Sanata mai wakiltar maza?ar Kano ta Kudu Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya bayyana cewa domin tabbatar da adalci da martaba dimukura?iyya ya kamata yankin Kudancin Najeriya ya samar da shugaban kasa na gaba a 2023 don yin adalci.

Sanata Gaya ya fadi hakan ne yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Abuja dangane da batun siyasa a shekarar za?e ta 2023 dake tafe.

Tsohon Gwamnan na Jihar Kano ya bayyana cewa Arewa ta samar da shugaban kasa na tsawon zango biyu wato shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda a cewarsa yayi namijin kokari wajen ci gaban kasar.

A cewar Sanatan, shugaban kasa Buhari na iya bakin kokarinsa a kan kasar. “Kan lamarin shugabancin kasa a 2023, zan marawa shugaban kasa daga yankin Kudancin kasar baya.

Lokaci yayi da ya kamata mu samu shugaban kasa daga yankin kudu yayinda Mataimakin shugaban kasa zai fito daga arewa. “Ina ganin ya kamata ayi adalci wajen juya shugabanci ta yadda mutane za su yi amanna da tsarin; daga arewa har kudu za su rungumi junansu.

Akwai bukatar Najeriya ya zama kasa daya. Kasa daya mai hadin kai,” in ji shi.

Kan kira ga sauya fasalin lamura, Gaya ya bayyana cewa ya kamata Najeriya ta ci gaba da kasancewa a matsayin kasa daya yayinda take inganta hanyar tattara kudaden shigarta.
“Allah ya san abunda yafi shiyasa ya sa mu a waje guda kuma nayi imani akwai dalilin hakan.

“Amma idan kace kana so ka sauya fasalin lamuran kasar ta hanyar amfani da kudaden shiga, cewa kowace jiha ta ci gashin kanta ko yankunan kasar suyi ta kansu, Ina ganin wannan ne tunanin wasu yan Najeriya.
“Amma Ina ganin cewa ya kamata Najeriya ta ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki daya,” in ji shi.

Dan majalisar ya nuna bukatar cewa ya kamata Najeriya tayi amfani da albarkatunta don ci gaban kasar.

Related posts

Leave a Comment