Za Mu Shafe Tarihin ‘Yan Ta’adda A Najeriya – Shugabannin Tsaro

Sabbin hafsoshin sojan Najeriya sun isa Maiduguri, babban birnin jihar Borno da niyyar ganawa da masu ruwa da tsaki don shawo kan yadda za a magance tayar da kayar baya a fagen daga.

Babban hafsan hafsoshin tsaro, Manjo Janar Leo Irabor ya jagoranci shugabannin hafsoshin zuwa hedikwatar rundunar tsaro ta rundunar Operation Lafiya Dole da ke Birnin Maiduguri da misalin a ranar Lahadi.

Wata babbar majiyar tsaro da ta bayyana wa wakilinmu cewa shugabannin rundunonin tare da sauran masu ruwa da tsaki ana sa ran za su yi tunani da sake dabarun yadda za su bullo da wata hanyar da za ta tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.

An ruwaito cewa dukkanin shugabannin hafsoshin da aka nada kwanan nan sun halarci taron. Ciki har da Shugaban hafsan hafsoshin tsaro, Manjo Janar Leo Irabor; Shugaban hafsan soji, Manjo Janar Ibrahim Attahiru; Shugaban hafsan sojin ruwa, Rear Admiral Awwal Gambo da shugaban hafsan sojin sama, Air Vice Marshal Isiaka Amao duk sun halarci taron.

Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya tarbe su a fadar gwamnatin jihar, inda suka ba da tabbacin shafe tarihin ‘yan ta’adda a yankin nan bada jimawa ba.

Related posts

Leave a Comment