Babar Kotun Jihar Kaduna ta bayar da umurni garkame asusun ajiyar bankuna goma 14 na Dan Majalisa Mai Wakiltar Doka da Gabasawa a Majalisar dokokin Jihar Kaduna, Hon. Haruna Inuwa Mabo, bisa samun sa da laifin cin Amana da zamba cikin aminci wajen yin keme-keme da kunnen uwar shegu wajen kin biyan dimbin basussuka da kudaden da ya amsa a hannun jama’a da sunan bashi.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Sakatariyar Lauya mai gabatar da ?ara Zainab Isiaka. A wani kwafin takardar da kotun ta tura ma daukacin bankunan goma 14 da Dan Majalisar Haruna Mabo ke amfani da su. Babbar kotun ta baiwa daukacin bankunan umurnin cewa, daga yanzu su damke duk wasu kudade da suka shigo asusun ajiyar Dan Majalisar domin yin amfani da kudaden wajen biyan dimbin basukan Al’umma da suke binsa har zuwa lokacin da adadin kudaden suka isa a biya dimbin jama’a hakkokinsu, sannan daga bisani a sakar masa ragamar asusun ajiyar sa.

Idan dai masu karatu basu mantawa ba, wannan ba shi ne karo na farko da jama’a ke zargin Dan Majalisar Haruna Mabo, da yin kunnen uwar shegu wajen kin biyasu hakkokinsu ba.
