Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya maida martani game da wasu kalamai da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi a kan tsige tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II daga Sarautar Kano.
Tsohon Gwamnan Kwankwaso ya fitar da jawabin da ya yi wa take da “Ganduje and the blabbering of an imposter” (Wato Ganduje da ?o?arin ?oye gaskiyar tarihi) ta bakin babban sakatarensa, Malam Muhammad Inuwa Ali.
Ya bayyana cewar “Hankalin Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ga wani tarin karya da kokarin juya tarihi kuru-kuru da gwamnan Kano da aka kakaba, Abdullahi Ganduje ya fito ya yi.”
Jawabin ya ce: “Abdullahi Ganduje ya yi wannan magana ne wajen kaddamar da littafin daya daga cikin shugabanninmu masu daraja, Goodluck Ebele Jonathan GCFR.”
“A ka’ida bai kamata kowa ya tanka mutum mai neman suna irin Ganduje ba, sai saboda cusa wasu ‘yan Najeriya masu daraja da ya yi, ya na neman ci masu mutunci.”
Sanata Rabiu Kwankwaso ya fara da taya tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan murnar rubuta littafi game da abin da ya faru da shi a mulki.
Kwankwaso ya ce: “Mun san cewa Ganduje ya na jin kan shi ba kowa ba a duk lokacin da yake tare da Sarkin, mun san cewa ya na da tsohuwar kiyayya da masarauta.”
Tsohon gwamnan ya ce a dalilin haka ne gwamnatin Ganduje ta fara da Sarki Muhammadu Sanusi II, aka nada Sarakunan da ba za a su iya takawa gwamnatinsa burki ba.
Sanata Kwankwaso ya kuma ambaci sukar cin bashin da gwamnatin Ganduje ta ke neman yi a wancan lokaci a matsayin abin da ya sa aka cirewa Sarkin na Kano rawani.
“Wannan shi ya kara sa aka tunbuke Sarki Sanusi II, babu abin da ya hada maganar da Jonathan.”
A kwanan nan baya kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta yi sababbin nade nade a masarautar karamar hukumar Karaye, kasar mahaifar tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso.
An nada mahaifin Kwankwaso mai suna Musa Saleh Kwankwaso, a matsayin ‘dan majalisar nadin sarakuna a masarautar Karaye.
