Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kisan mutane bakwai, bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai kan al’ummar Gora Gan da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar.
Wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, ya ce lamarin ya faru ne a daren ranar Alhamis.
“Jami’an tsaron da ke gudanar da ayyukan tsaro na cikin gida a wasu sassan kudancin jihar Kaduna sun bayanna cewa an auka wa al’ummar Gora Gan da ke karamar hukumar Zangon Kataf a daren Alhamis.
“Hukumomin tsaro, wadanda suka hada da sojoji da ‘yan sanda, sun bayanna cewa an auka wa garin na Gora Gan ta fuskoki da dama, ciki har da yankin kasuwa da gidajen da ke shimfidawa zuwa yankin Tudun Wada na Gora Gan,” in ji shi.
Mista Aruwan ya ce sojojin sun fatattaki maharan, sun daidaita yankin baki daya sannan sun tsamo gawarwakin mutane bakwai wadanda suka hada da Peter Akaho (70), Ayuba Steven Sheyin (67), Jummai Ayuba (55), Ishaya Joel (35), Yakubu Saviour (14) , Ayuba Goodluck (11) da Patience Ayuba (6).
“Jami’an tsaro sun ci gaba da bayar da rahoton cewa mutum daya ya ji rauni a hare-haren, yayin da gidaje 13 da shaguna biyu suka kone a harin.
“Sojojin Operation Lafiya Dole (OPSH), Dakarun na Musamman na Hedkwatar Tsaro da jami’an ‘yan sanda suna bin sawun maharan”.
Gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yiwa ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba a matsayin na dabbanci da rashin mutuntaka, sannan ya aika da ta’aziyya ga dangin da suka rasa‘ yan uwansu ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan su.
Gwamnan ya kuma umarci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar, SEMA, da ta yi lissafin barnar da aka tafka tare da samar da kayayyakin tallafi nan take.
Mista Aruwan ya kuma ce Gwamnatin Jihar Kaduna ta samu rahoton harbi lokaci-lokaci a kan hanyar Fadan Kagoma-Kwoi a karamar hukumar Jema’a. An harbi wani direba, amma yanzu an daidaita shi.
Gwamnan ya bayar da umarnin a gudanar da bincike kan musabbabin harbe-harben.
