Lalacewar Tsaro: Ya Wajaba Buhari Ya Sauka – Dr Gumi

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan a Najeriya, Shaikh Ahmad Abubakar Gumi ya bukaci Shugaba Buhari ya yi murabus tunda ya kasa tsare rayukan al’umma.

Kiran Shaikh Gumi na zuwa ne bayan kisan gillar da ’yan Boko Haram suka yi wa manoma 43 a garin Zabarmari da ke Jihar Borno.

Malamin ya ce kashe-kashen da ake yi a Gwamnatin Buhari ya ninka na gwamnatin da ta gabata, don haka babu wani uzuri da za a ci gaba da yi wa gwamnatin.

Shaikh Ahmad Gumi ya koka kan yadda ya ce kullum rayukan wadanda ba su ji ba, ba su gani ba na salwanta saboda gazawar gwamnati mai ci.

Tun bayan kisan gillar da Boko Haram ta yi wa Manoman Shinkafa a ?auyen Zabarmari dake karamar Hukumar Jere ta Jihar Borno a ?arshen Mako, shugaban ?asa Buhari ke cigaba da fuskantar suka a ciki da wajen Najeriya, inda ake ganin gazawarshi ta haifar da ta?ar?arewar tsaro a ?asar.

Malaman addini wa?anda a baya suka kasance masu goyon bayan shugaban a yanzu sun janye gaba ?aya, inda suka ke sukar shugaban ba ?a??autawa.

Related posts

Leave a Comment