Zuciya ta na cike da bakin ciki da kunci saboda kisan gillar da aka yiwa manoma 43 a Zabarmari na jihar Borno, hakika zuciya ta na tare da ‘yan uwa da abokan arziki na wadannan bayin Allah da aka kashe su kisan zalunci ba tare da hakki ba.
Na sami wannan mummunan labari cikin yanayi na kaduwa da tashin hankali, kasancewar babu wata hujja ko dalili da za a iya fakewa da shi a aikata irin wannan danyen aiki, walau a addinance ko wata akida ta daban a jinsin dan adam.
Hakika abin da Boko Haram suka aikata kan wadannan manoma da basu jiba basu gani ba ya kai mutukar muni da abin kyama ga dukkan wani dan Adam da yake da cikakken hankali da tunani.
Ina mutukar Allah wadai da takaici wannan mummunan abun kyama wanda kowacce irin al’umma mai ilimi da sanin hakki zata yi tir da shi.
Babu shakka dukkan ‘yan Najeriya suna cikin bakin ciki da alhinin wannan babbar wauta da babu wani addini a duniya da zai goyi bayan ta.
Ina kuma mika sakon ta’azziya ga gwamnati da al’ummar jihar Borno da kuma dangin wadannan bayin Allah da dukkan ‘yan Najeriya, bisa wannan mummunan abin bakin ciki.
Ina kuma kira ga jami’an tsaro su kara kaimi wajen tunkarar matsalolin tsaron dake addaba sassan Najeriya, sannan ina kira ga ‘Yan Najeriya su ci gaba da bawa jami’an tsaro hadin kai domin kawo karshen wannan matsala.
Dole sai mun hada kai zamu ga bayan ta. -Atiku Abubakar
Allah Ya sauwake
