Samar Wa Matasa Aiki Ne Zai Kawo ?arshen Zanga-Zanga – Lawan

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya yi gargadin cewa Naeriya na iya fuskantar sabuwar zanga zanga idan gwamnati ta gaza magance rashin aikin yi na matasa. Lawan ya yi gargadin ne a jiya litinin
yayin wani zaman kare kasafin kudin 2021 na ma’aikatar noma a majalisar dokokin tarayya.


Matasan Najeriya fiye da 10,000 ne suka gudanar da zanga zangar EndSARS a fadin kasar kwanan nan, inda suka nuna fushinsu a kan cin zarafin mutane da yan sanda ke yi da kuma rashin shugabanci nagari, lamarin da ya ja hankalin gwamnati sosai inda nan take gwamnatin ta biya masu bukatunsu na soke rundunar SARS. Lawan ya bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakai a aikace wajen shigar da matasa a kasafin 2021.

“Ya kamata kasafin kudinmu na 2021 ya mayar da hankali ne wajen samar wa matasan Najeriya damar ayyukan yi. “Sun gudanar da zanga-zanga saboda iya abun da za su iya yi ke nan, wasunsu kuma ba su iya shiga an yi da su ba amma suna tare da masu yi. “Mu yi kokari mu same su a inda suke. Ba sai mun jira har sai sun yi kokarin zanga zanga ba. Mu dauki mataki. Mu isa garesu kuma suna a yankunan karkara ne. Mafi akasarinsu. “Don haka mu same su a chan. Mu basu abunda za mu iya da kuma abunda suke bukata, wannan ita ce hanya daya tilo da za mu bi”, inji shi.

”Shugaban Majalisar ya bayyana Ma’aikatar Noma ta Tarayya a matsayin wadda za ta kawo sauyi a Najeriya. Ya ce ma’aikatar na da damar samar da ayyukan yi da bangaren mai ba zai iya samar wa mutane ba sai ‘yan tsiraru. Ma’aikatar noma na da kasafin kudin naira biliyan 139 a 2021.

Amma Shugaban kwamitin majalisa kan noma, Abdullahi Adamu, ya ce kasafin kudin ya yi karanta sannan ya yi kira ga gwamnati da ta samar da manufofin da zai kawo sauyi a bangaren noma.

Related posts

Leave a Comment