Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da cewa ba zai gabatar da jawabi ga ‘yan Nijeriya a dandalin Eadle Square kamar yadda ya yi niyya a baya ba. Haka zalika, shugaban kasar ya sanar da cewa, a yanzu zai gabatar da jawabin ne kai tsaye ga ‘yan kasar ta talabijin daga fadar shugaban kasa.
Femi Adesina, babban hadiminsa ta fuskar watsa labarai, ya fitar da sanarwa kan cewar Buhari zai gabatar dan jawabin ne da misalin karfe 7 na safiyar yau Alhamis ranar 1 ga watan Oktoba, 2020.
A cikin sabuwar sanarwar, Adesina ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da waccan sanarwar ta baya, wacce ta nuna shugaban kasar zai gabatar da jawabin kai tsaye daga Eagle Square, Abuja.
Haka zalika, ya bayyana cewa, da zaran shugaban kasar ya gama gabatar da jawabin na sa, zai wuce kai tsaye dandalin Eagle Square, wajen taron cikar Nigeria shekaru 60 da samun ‘yanci.
Sai dai bikin ranar ‘yancin kan a bana ba zata yi armashi kamar yadda aka saba gani a shekarun baya ba, dalilin fama da matsala ta cutar CORONA da ta addabi duniya.
